Ran 19 ga wata, ofishin kula da harkokin 'yan gudun hijira na MDD da ke kasar Cote d'Ivoire ya nuna cewa, saboda halin da gidan kasar Liberia ke ciki ya shiga ruwan sanyi, yanzu 'yan gudun hijira da yawa na Liberia sun dawo gida daga Cote d'Ivoire.
Jami'in ofishin ya bayyana cewa, a cikin watan baya, akwai 'yan gudun hijira fiye da dubu 5.1 suka bar Cote d'Ivoire suka dawo gida.
Saboda yakin basasa wanda ya shafi shekaru 14 na kasar Liberia, akwai 'yan gudun hijira kusan dubu 400 suka je makwabcin kasar. A kasar Cote d'Ivoire akwai 'yan gudaun hijira fiye da dubu 50. [Musa]
|