A ran 19 ga wata a birnin Bissau, babban birnin kasar Guinea-Bissau, a gun wani manema labaru da aka shirya, ministan harkokin gida na kasar Guinea-Bissau Mumine Embalo ya bayyana cewa, magoya bayan tsohun shugaban kasar Kumba Yala sun yi kulle kullen kai farmaki ga ma'aikatar harkokin gida ta kasar a makon jiya.
Mr Embalo ya ce, wani 'dan majalisar jam'iyyar Social Renovation Party da ke goyon bayan Kumba Yala ya yi kulle kullen kai farmakin, haka kuma wannan 'dan majalisar ya ba da kudi domin wannan matakai da aka dauka.
A ran 16 ga wata da alfijir, wasu mutane wadanda ba a san asalinsu ba sun kai farmaki ga ma'aikatar harkokin gida ta kasar, wannnan ya sa 'yan sanda biyu sun mutu yayin da sauran mutane fiye da goma suka ji rauni.(Danladi)
|