
A ran 18 ga wata, an yi babban taron MDD, inda aka yi muhawara a kan shirin kudurin habaka kwamitin sulhu da gamayyar kasashen Afirka ta gabatar a makon jiya.
A gun muhawarar, wakilan kasashen Nijeriya da Masar da Aljeriya da Burkina faso sun yi jawabi, inda suka nemi a kawo karshen rashin kasancewar zaunannun kujerun kasashen Afirka a kwamitin sulhu, kuma suka yi kira ga kasashe daban daban da su goyi bayan shirin kudurin da gamayyar Afirka ta gabatar.
A cikin shirin kudurin da gamayyar Afirka ta gabatar, ana neman kara zaunannun kasashe 6 wadanda ke da ikon nuna rashin amincewa da kuma kasashe 5 da ba na dindindin ba a kwamitin sulhu.
A halin yanzu, gamayyar Afirka ba ta fitar da kasashen da za su nemi kujerar dindindin a kwamitin sulhu a madadin kasashen Afirka ba. Amma kasashen Masar da Afirka ta kudu da Nijeriya da kuma Kenya sun riga sun nuna sha'awarsu game da aikin nan.(Lubabatu Lei)
|