A ran 18 ga wanann wata, an yi bikin budewar taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Afrika da kasar Amurka a birnin Dakar, hedkwatar kasar Senegal.
A gun taron dandalin tattaunawa da aka shriya, za a mai da hankali ga yin tattaunawa kan halin da ake ciki na aiwatar da shirin dokar da tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton ya sa hannu a kai a shekarar 2000 game da karuwar da kasashen Afrika suka samu da damar da aka samar musu, don ci gaba da kawar da katangar da aka gitta ga harkokin cinikayya da ba da himma ga raya masana'antu masu zaman kansu da sa kaimi ga kasashen Afrika da ke kudancin Sahara wajen yin ficin cinikayya zuwa kasar Amurka.
A watan Mayu na shekarar 2000, gwamnatin Clinton ta sa hannu kan shirin doka game da karuwar da kasashen Afrika suka samu da damar da aka samar musu, inda aka karfafa cewa, za a kara inganta huldar da ke tsakaninta da kasashen Afrika da ke kudancin Sahara ta hanyar yin cinikayyya.(Halima)
|