Bisa labaran da kafofin yada labarai na kasar Kamaru suka bayar ran 17 ga wata,an ce kwanan baya bankin duniya ya tsai da kudurin ba da kudin dalar Amurka miliyan 677.8 domin taimaka wa Nijeriya da Madagascar da kuma Benin wajen yakar talauci.
A ran 16 ga wata wakilin bankin duniya ofishin da ke wakilatar bankin duniya a Abuja ya bayyana cewa bankin duniya zai ba da sabon rancen dalar Amurka miliyan 390 ga kasar Nijeriya wadda ta fi yawan mutane a Afrika wajen tabbatar da shirin taimakawa matalauta.manufar Nijeriya wajen yaki da talauci ita ce rage talauci da samun tattalin arziki na sifoffi daban daban da tafiyar da harkokin mulki yadda ya kamata.
Bankin duniya ya kuma ba da rance mai gatanci na dalar Amurka miliyan 257.8 ga Madagascar ta kungiyar neman bunkasuwa ta duniya.(Ali)
|