A jiya ran 17 ga wata, a birnin New York, ministocin harkokin waje na gamayyar kasashe hudu da ke kunshe da Japan da Jamus da India da Brazil wadanda ke neman kujeru a kwamitin sulhu na MDD sun yi shawarwari tare da wakilan wasu kasashen gamayyar Afirka a kan maganar habaka kwamitin sulhu na MDD, amma duk da haka, ba su samu daidaituwar baki ba.
An ce, za a ci gaba da shawarwarin a mako mai zuwa a birnin Geneva, a sa'i daya kuma, wakilan wadannan kasashe a MDD za su ci gaba da yin shawarwarin.
Daga bangaren kawancen kasashen Afirka, ministocin harkokin waje ko wakilai na Nijeriya da Lybia da Afirka ta kudu da kuma Masar sun halarci shawarwarin. Gamayyar kasashe hudu suna fatan za a jefa kuri'a a kan shirin habaka kwamitin sulhu da suka gabatar a gun babban taron MDD a watan da muke ciki, amma idan ba su sami goyon baya daga wajen kasashen Afirka ba, to, da wuya za su sami sama da kashi biyu bisa uku na kuri'un.(Lubabatu Lei)
|