
A ran 13 ga wata a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal, shugaban kasar Abdoulaye Wade ya bayyana cewa, shugabannin kasashen Afirka sun yarda da shawarar da shugaban zartaswa na kawancen kasashen Afirka kuma shugaban kasar Nijeriya Obasanjo ya gabatar, sun yanke shawarar gina wata babbar koriyar katanga a yankin Sahara.
Mr Wade ya ce, za a gina koriyar katanga mai fadin kilomita 5 daga birnin Dakar na kasar Senegal zuwa kasar Djibouti wadda ta ratsa kasashen Senegal da Mali da Niger da Chadi da Sudan da Habasha da kuma Djibouti. Sabo da haka ne, kasashen da abin ya shafa za su bayar da kayayyaki da kudi da kuma mutane domin dasa itace, ta yadda za a hana yaduwar hamadar Sahara da moriyar 'ya 'yansu.(Danladi)
|