Wakilan sojan gwamnatin kasar Cote d'Ivoire da tsohuwar kungiyar dakarun da ke adawa da gwamnatin wato jam'iyyar the New Forces sun yi shawarwari a birnin Yamoussoukro, hedkwatar kasar Cote d'Ivoire a ran 7 ga watan nan, inda suka yi tattaunawa kan maido da shirin kwance damara.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, babban makasudin shawarwarin da aka yi a ran nan shi ne tabbatar da jadawalin kwance damara. Bangarorin 2 da suka yi shawarwarin sun amince da kafa kwamitoci guda 2 na musamman, don sa idon kan kwance damara da tsara matakan tabbatar da lafiyar wakilan jam'iyyar the New Forces da suka shiga gwamnatin sulhuntawar al'ummar kasar. Wakilan sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da na kasar Faransa sun halarci shawarwarin nan.?Tasallah?
|