
Ran 7 ga wata, Mr.Ramgoolam sabon firayin ministan kasar Mauritius ya nada membobin gwamnatin 19, ya kafa sabuwar gwamntai bayan babban zabe na majalisar kasar da aka yi a ran 3 ga wata. Sabuwar gwamnatin ta rantsar da aiki a maraice a babban birnin kasar.
Ofishin shugaan kasar Mauritius ya bayar da sanarwar cewa, duk membobin sabuwar gwamnatin su zo daga kungiyar tarrayar jam'iyyun adawa da ke karkashin jakorancin Ramgoolam, a cikinsu Ramgoolam ya zama ministan tsaron kasa kuma na harkokin gida, Madan Dulloo ya zama ministan harkokin waje, Rama Sithanen ya zama ministan sha'anin kudi da na tattalin arziki. [Musa]
|