|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-07-06 12:09:19
|
An samu kwanciyar hankali a yankin yammacin Afirka, in ji M.D.D.
cri
Wakilin musamman na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da ke yammacin Afirka Ahmedou Ould-Abdallah ya bayyana a birnin Dakar, hedkwatar kasar Senegal a ran 5 ga watan nan cewa, a kwanan baya an samu kwanciyar hankali a yankin yammacin Afirka.
A ran nan shugabannin kungiyoyin musamman na Majalisar Dinkin Duniya da suke kiyaye zaman lafiya a kasashen Sierraleone da Cote d'Ivoire da Liberia da kuma Guinea-Bissau sun yi taro a asirce a birnin Dakar, inda suka yi nazarin halin da yammcin Afirka ke ciki da kuma ci gabansa.(Tasallah)
|
|
|