Kwamitin kula da tattalin arziki na kasashen Afirka na Majalisar Dinkin Duniya da babban zaurensa yake birnin Addis Abeba, hedkwatar kasar Habasha ya ba da wata sanarwa a ran 5 ga watan nan, inda ya yi fatan taron shugabannin rukunin kasashen G8 masu arzikin masana'antu zai sa kaimi ga kasashen Afirka wajen tabbatar da makasudin bunkasuwar shekaru dubu da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara.
Sanarwar nan ta jaddada cewa, kawar da talauci daga kasashen Afirka, ba ma kawai yana bukatar kara ba da taimako ba, har ma ya kamata a ba da taimako yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, ta yi kira ga kasashe masu ci gaban masana'antu da su cika alkawarinsu na ba da taimako ga kasashen Afirka tun da wuri a gun taron shugabannin rukunin kasashen G8 da za a yi, kuma su dauki matakan sa kaimi ga kasashen Afirka wajen gaggauta aikin tabbatar da makasudin bunkasuwar shekaru dubu.(Tasallah)
|