Mai kula da kwamitin babban zabe mai zaman kansa na kasar Burundi Paul Ngarambe ya bayyana a ran 5 ga watan nan cewa, tsohuwar kungiyar dakarun kabilar Hutu da ke adawa da gwamnatin wato jam'iyyar Forces for the Defence of Democracy ta ci nasara a cikin zaben 'yan majalisar da aka yi a ran 4 ga watan nan.
Mr. Ngarambe ya kara da cewa, bisa kuri'un da aka kidaya a yanzu da yawansu ya kai kashi 80 bisa dari, jam'iyyar Forces for the Defence of Democracy tana gaban sauran jam'iyyun kasar bisa matsayin rinjaye. Wannan ya nuna cewa, jam'iyyar Forces for the Defence of Democracy ta ci nasara a cikin babban zaben da aka yi a karo na farko ta hanyar dimokuradiyya a kasar Burundi bayan da yakin basasa ya barke a shekarar 1993.(Tasallah)
|