Bisa labarin da muka samu daga gidan TV na kasar Cameroon a ran 4 ga wata da yamma, an yi wani bala'in nutsewar jirgin ruwa a teku kusan Cameroon, a kalla dai mutane 30 suka mutu.
Wannan jirgin ruwa ya tashi daga Nijeriya, kuma zai tafi Gabon. Lokacin da bala'in ya faru, akwai fasinjoji daga kasar Nijeriya, Mali, Benin da sauran kasashen yammancin Afirka fiye da 60 suna jirgin ruwa.
Bayan nutsewar jirgin ruwa, an ceta fasanjoji kamar 30, amma ba a sami sauran fasinjoji ba. yanzu, ana cigaba da aikin ceto. Kuma ana bincike asalin bala'in. [Musa]
|