
Ran 5 ga wata, Mr.Jugnauth shugaban kasar Mauritius ya nada Mr.Ramgoolam shugaban jam'iyyar Leba ya zama sabon firayin ministan kasar.
Ofishin shugaba ya bayar sanarwar cewa, shugaban kasar ya nada Ramgoolam ne bayan firayin minista na yanzu Mr.Berenger ya yi murabus.
Daga baya Mr.Ramgoolam ya yi jawabi a TV. Ya yi kira ga jama'ar kasar da su yi hadin kansu don goyon baya sabuwar gwamnati. Ya ce aikin musamman na gwamnatin shi ne samar da aikin yi, bunkasa masana'antun fito da sukari da na saka. [Musa]
|