
An rufe taron 5 na shugabannin Kawancen Kasashen Afirka da aka yi yini 2 ana yinsa a birnin Syrte na kasar Libya a ran 5 ga watan nan. A gun wannan taro, an tabbatar da matsayin bai daya da kasashen Afirka suke tsayawa kan kawar da talauci daga kasashen Afirka da kuma yin wa Majalisar Dinkin Duniya kwarkwarima.
Game da yin wa Majalisar Dinkin Duniya kwarkwarima, taron nan ya tsai da kudurin cewa, kasashen Afirka sun nemi samun zaunannun kujeru guda 2 tare da ikon kin amincewa, da kuma guda 5 da ba na zaunannu ba a kwamitin sulhu na majalisar.
Game da fama da talauci a Afirka, kungiyar AU ta nanata a cikin kudurin da ta yi cewa, za ta ci gaba da daukan matakai wajen kawar da talauci daga yankin nan, amma tana bukatar gama kanta da gamayyar kasashen duniya wajen neman samun bunkasuwa. Ban da wannan kuma, kudurin nan ya gabatar da wasu shawarwari kan raya kasashen Afirka.(Tasallah)
|