Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-07-05 17:02:19    
Firayin ministan kasar Mauritius ya yi murabus daga mukaminsa

cri
A ran 5 ga wata da safe, firayin minista mai ci na kasar Mauritius Mr. Paul Berenger ya mika wa shugaban kasar Mr. Anerood Jugnauth takardar yin murabus daga mukaminsa domin kawancen jam'iyyun da ke rike da karagar mulkin kasar da ke karkashin jagorancinsa ya ci hasalar zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka yi a ran 3 ga wata.

Bisa sakamakon da aka bayar a ran 4 ga wata, kawancen jam'iyyun da ke rike da karagar mulkin dokokin kasar da ke jagorancin Berenger ya samu kujeru 22 kawai daga cikin dukkan kujeru 62 na majalisar. Amma kawancen jam'iyyun da ke adawa da gwamnatin yanzu kuma ke karkashin jagorancin Navin Ramgoolam ya sami kujeru 38. Sabo da haka, Mr. Navin Ramgoolam wanda yake da shekaru 57 da haihuwa kuma ya taba hawa kan mukamin firayin ministan kasar tun daga shekarar 1995 zuwa shekarar 2000 zai sake kama kan mukamin firayin ministan kasar. (Sanusi Chen)