A birnin Syrte na kasar Libya, shugaban kwamitin Kawancen Kasashen Afirka Alpha Oumar Konare ya bayyana a ran 4 ga watan nan cewa, kudurin yafe wa kasashen mafi fama da talauci guda 18 basussukan da ake binsu da rukunin kasashen G8 masu arzikin masana'antu ya tsai da a kwanan baya, wani muhimmi da madaidaicin mataki ne da ya dauka, abin da ake fuskanta a yanzu shi ne tilas ne kasashe masu arzikin masana'antu su cika alkawarin da suka yi cikin tsanake.
Mr. Konare ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi jawabi a gun bikin bude taron na 5 na shugabannin kungiyar AU a ran nan. Ya kara da cewa, ya kamata nan gaba a sa ido kan kasashe masu arzikin masana'antu wajen cika alkawarin da suka yi yadda ya kamata.
A sa'i daya kuma, a gun bikin bude taron, shugaban kasar Libya Muammar Al-Qadhafi ya bayyana cewa, kasashen Afirka sun yi wa kasashe masu ci gaban masana'antu godiya saboda taimakonsu, amma sun ki karbar taimakon da za a ba su tare da sharadi.(Tasallah)
|