
Babban sakataren mai cikakken iko na kungiyar ECOWAS Mohamed Ibn Chambas, wanda ke halartar taro na 5 na shugabannin kungiyar AU a birnin Syrte na kasar Libya, ya bayyana a ran 4 ga watan nan cewa, ya kamata bangarori daban daban na kasar Guinea-Bissau su maganci harkokin nuna karfin tuwo a cikin babban zaben shugaban kasar da za a gudanar a zagaye na 2 a ran 24 ga watan nan.
Sa'an nan kuma, Mr. Chambas ya kalubalanci sojojin kasar Guinea-Bissau da su tsaya matsayin 'yan ba-ruwanmu a cikin kada kuri'a a zagaye na 2 da za a yi, ya kuma yi kira ga bangarorin da suka shiga babban zaben da su girmama sakamakon babban zaben. Ban da wannan kuma, ya yi kashedi cewa, idan ana samun tashin hankali a kasar Guinea-Bissau, to, zai ba da tasiri kan kwanciyar hankali na duk yankin yammacin Afirka kai tsaye.(Tasallah)
|