Ran 4 ga wata, kungiyar wakilan Majalisar dinking duniya ta bayyana cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya sun kai aikin soja ga dakaru masu yin adawa da gwamnatin Ruwanda wadanda ke boye a cikin kungurmin daji da ke lardin Sud-Kive na gabashin Kongo Kinshasa.
Bisa labarin da muka samu, makasudin aikin soja shi ne kori dakaru masu yin adawa da gwamnatin Ruwanda, saboda a kwanakin baya sun kan kai farmaki ga farar hula na Kongo Kinshasa.
Sojojin kiyaye zaman lafiya da sojojin gwamnatin kasar Kongo Kinshasa fiye da dubu hudu sun halarci aikin soja. [Musa]
|