Ministan harkokin waje na kasar Sudan Mustafa Othman Ismail da ke halartar taron shugabannin Kawancen Kasashen Afirka a birnin Syrte na kasar Libya ya bayyana a ran 4 ga watan nan cewa, yin wa Majalisar Dinkin Duniya kwarkwarima ya shafi moriyar bangarori daban daban, shi ya sa tilas ne a yi taka tsantsan wajen wannan.
Lokacin da yake zantawa da manema labaru a ran nan, Mr. Ismail ya jaddada cewa, ya kamata kasashen Afirka su sami kujerun din din din guda 2 a kwamitin sulhu na majalisar, sa'an nan kuma kasashen da aka kara a wannan gami su iya kin amincewa. Ya ci gaba da cewa, kasashen Afirka sun riga sun tattauna wannan batu a gun taron ministocin harkokin waje na kungiyar AU da aka yi kafin wannan, za su mika sakamakon karshe a gun taron shugabannin kungiyar AU da ake yi don kada kuri'a.(Tasallah)
|