Kwamitin babban zabe na kasar Mauritius ya ba da sanarwa a ran 4 ga watan nan da dare cewa, kawancen 'yan hamayya wato 'kawancen al'ummar kasar' da jam'iyyar kwadago ke shugabanta ya ci nasarar zaben 'yan majalisar jama'ar kasar da aka yi a ran 3 ga watan nan.
Shugaban jam'iyyar kwadago Navin Ramgoolam zai sake zaman firaministan kasar bayan shekaru 5 da suka wuce, zai fara wa'adin aikinsa na shekaru 5. Shugaban kawancen rike da mulki na kasar kuma firaministan kasar na yanzu Paul Berenger zai zama dan majalisar jama'ar kasar a wannan gami. A cikin jawabin da ya yi a ran nan da dare, Mr. Berenger ya amince da cin tura, zai yi murabus nan da nan bayan da aka bayar da sakamakon babban zaben.(Tasallah)
|