Shugaban Kawancen Kasashen Afirka kuma shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana a ran 4 ga watan nan cewa, gwamnatin kasarsa ba za ta koma da tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor da ke gudun hijira a kasar saboda lambar da kasashen duniya suka matsa mata ba.
Mr. Obasanjo ya jaddada cewa, kasashen duniya sun amince da kudurin da gwamnatinsa ta tsai da a shekarar 2003 kan ba da mafaka ta siyasa ga Mr. Taylor. A sa'i daya kuma, ya nanata cewa, gwamnatin kasar Nijeriya ba za ta koma da Mr. Taylor ba, kuma ba za ta mika wannan magana a gaban kungiyar AU ko kungiyar ECOWAS don yin tattaunawa ba, sai gwamnatin farar hula ta kasar Liberia ta bukata.(Tasallah)
|