Ran 4 ga wata, jakadan kasar Sin da ke kasar Niger ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ba da taimakon kudi na dalar Amurka dubu dari 3 don taikamaki kasar Niger a wajen yaki da yunwa.
A ran 2 ga wata, kasar Sin ta taba ba da kudin dalar Amurka dubu dari 2 ga Niger. Wannan ya zama karo na biyu ne da kasar Sin ta bayar da taimakon kudi ga kasar Niger.
Chen Gong, jakadan kasar Sin da ke kasar Niger ya yi nuni da cewa, burin da kasar Sin ta sa gaba shi ne a bayar da goyon baya ga gwamnatin kasar Niger a wajen yaki da matsalar kalancin abinci, ta yadda za a sassauta halin kaka nika yi da mutanen kasar ke ciki. [Musa]
|