A kwanan baya, firayin minista Ali Mohammed Gedi na gwamnatin rikon kwarya ta kasar Somaliya ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta bi shirin neman sulhu gaba daya a duk fadin kasar domin ingiza aikin shimfida zaman lafiya da dinkuwar duk kasar tun da wuri.
Lokacin da yake ganawa da manema labaru a wani ofishin wucin gadi a garin Jowhar da ke arewa da birnin Mogadishu na kasar, Mr. Gedi ya ce, a cikin makon da ake ciki, a yankuna 92 na duk kasar Somaliya, za a shirya tarurukan neman sulhu domin kafa ene ene a wadannan yankuna. Bayan watanni 2 masu zuwa, za a kira taron neman sulhu a larduna daban-dabam. Daga karshe, za a kira babban taron neman sulhu a duk fadin kasar a birnin Mogadishu, babban birnin kasar. (Sanusi Chen)
|