Lokacin da yake zantawa da kafofin yada labaru a ran 3 ga watan nan da dare, shugaban kasar Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ya bayyana cewa, ko da yake jam'iyyar ANC da ke mulkin kasar tana da matsayin rinjaye na samun kujaru da yawansu ya kai kashi 2 bisa 3 a cikin majalisar dokokin kasar, amma ba za ta gyara tsarin mulkin kasar don ya ci gaba da zaman shugaban kasar a karo na 3 ba.
Game da tambayar mutumin da zai zama shugaban kasar da kuma shugaban jam'iyyar ANC, Mr. Mbeki ya jaddada cewa, wannan yana dogara ga ra'ayoyin jama'ar kasar da dukan 'yan jam'iyyar ANC, ban da wannan kuma, yana ganin cewa, ba zai yiwu a warware wannan matsala kafin taron wakilan jam'iyyar ANC da za a yi a shekarar 2007 ba.(Tasallah)
|