Bisa labarin da kafofin yada labaru na kasar Cote d'Ivoire suka bayar a ran 24 ga watan nan, an ce, wakilin Kawancen Kasashen Afirka da ke kasar Liberia Noumou Diakite ya ba da wata sanarwa a birnin Conakry, hedkwatar kasar a kwanan baya cewa, ya zuwa yanzu sojoji fiye da dubu dari sun kwance damara a kasar.
Mr. Diakite ya bayyana cewa, yanzu gwamnatin rikon kwarya ta kasar Liberia tana nan tana tattara kudi don komar da sojojin da suka kwance damara da sake tsugunar da su. Ya kuma fayyace cewa, abun gaggawa da kasar Liberia za ta yi shi ne kafa wata sabuwar rundunar soja ta gwamnatin kasar don maye gurbin sojojin kiyeye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, bisa yarjejeniyar zaman lafiya ta Accra.(Tasallah)
|