A ran 24 ga wata, hadadden kwamitin zabe mai zaman kai na kasar Afirka ta tsakiya ya shelanta a hedkwatar kasar, Bangui cewa, shugaban kasar mai ci Farancois Bozize ya samu kuri'un da yawansu ya kai kashi 64.6% a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ran 8 ga wata a zagaye na biyu, sabo da haka, ya zama shugaban kasar, wa'adin aikinsa zai kai shekaru 5.
Bisa sakamakon zaben da kwamitin ya bayar, an ce, yawan kuri'un da Mr.Bozize ya samu ya wuce kuri'un da aka kada wa abokin takararsa kuma tsohon firayin ministan kasar Martin Ziguele kwarai.
Zaben nan zai kammala mulkin rikon kwarya da Mr.Bozize yake yi a kasar bayan da ya yi juyin mulkin soja a watan Maris na shekarar 2003, ta yadda za a maido da tsarin mulki a jamhuriyar Afirka ta tsakiya kamar yadda ya kamata.(Lubabatu Lei)

|