Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-25 09:22:49    
Kungiyar EU ta ba da taimakon kudi ga Guinea?Bissau don gudanar da babban zabe

cri
Ran 24 ga watan nan, wani jami'in gwamnatin kasar Guinea?Bissau ya tabbatar da cewa, Kawancen Kasashen Turai ya amince da ba da taimakon kudi da yawansa ya kai kudin euro miliyan 9 ga gwamnatin kasar Guinea-Bissau domin gudanar da babban zaben shugaban kasar lami lafiya, wanda za a yi a watan gobe.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, za a yi amfani da wannan kudi ne wajen shirya babban zaben shugaban kasar da biyan kudi ga 'yan kallo 100 da Kawancen Kasashen Turai zai tura da kuma biyan albashi ga ma'aikatan gwamnatin kasar da rundunar soja da aka jinkirtar da biyansu. Wani jami'i daban na kasar Guinea?Bissau ya bayyana cewa, idan an gudanar da babban zaben shugaban kasar lami lafiya a wannan gami, to, mai yiwuwa ne kawancen zai kara ba da taimakon kudi da yawansa zai kai kudin euro miliyan 9 a karshen watanni 6 na wannan shekara.(Tasallah)