Ran 24 ga wata, gwamnatin kasar Kenya ta tabbata cewa, ambaliyar da ke faru a yammacin kasar tun daga kashen makon da ya wuce ta riga ta kashe mutane 4, kuma mutane darurruka sun rasa gidajensu.
Amadi jamii mai kula da harkokin balai na gwamnatin kasar ya ce, an yi ruwan sama da yawa a yankin kusa da tabkin Victoria, wasu koguna?sun yi cikowa. Har yanzu an riga an tabbata cewa mutane 4 sun mutu a ambaliyar ruwa, kuma darurruka sun rasa gidajensu. [Musa]

|