A dai dai lokacin da 'ranar nahiyar Afirka' ke kusantowa, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya nanata a ran 24 ga watan nan cewa, Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da goyon bayan ayyuka daban daban na kasashen Afirka, ta yadda za ta sa kaimi kan yalwata kasashen Afirka daga dukan fannoni.
A cikin wata sanarwar da ya bayar, Mr. Annan ya bayyana cewa, a shekarun nan da suka wuce, an samu canje-canje masu yawa a nahiyar Afirka a jere, amma ana fuskantar kalubale na hargitsin dakaru da talauci da kuma ciwace-ciwace. Ya kara da cewa, shekarar 2005 tana da muhimmanci ga kasashen Afirka, yana fatan kasashen duniya za su kara mai da hankulansu kan Afirka a fannonin neman samun zaman lafiya da bunkasuwa a gun taron manyan shugabanni na majalisar da za a yi a watan Satumba na shekarar da muke ciki.(Tasallah)

|