Ran 16 ga wata da dare, jam'iyya mai mulkin kasa ta bayar da sanarwa cewa, ta ci nasara a babban zabe na uku na majalisar kasar.
Sanarwar ta ce, jam'iyyar ta ci nasara a lardin kudu, larin Oromia, lardin Amhara da lardin Tigray, shi ya sa ta sami yawancin kujerun majalisar, kuma za ta kafa sabuwar majalisar ministoci cikin kajeran lokaci.
Bisa tsarin mulkin kasar, majalisar ta kunshe da membobi 547, ko shekaru 5 za a sake yi babban zabe, jam'iyyar wadda ta sami yawancin kujeru za ta kafa majalisar ministoci.[Musa]
|