
A ran 15 ga watan nan da dare, an sa aya ga ayyukan jefa kuri'u na zaben 'yan majalisun jihohi bakwai da na majalisar wakilan jama'ar tayyarar kasar Habasha. Wannan shi ne karo na uku da aka yi zaben dimokuradiyya tsakanin jam'iyyu daban daban a cikin tarihin kasar Habasha.
Jam'iyyu 36 gaba daya sun shiga babban zaben, a cikinsu, jam'iyyu uku mafi muhimmancin su ne jam'iyyar EPRDF da kawancen karfin dimokuradiyya na Habasha da kuma kawancen dimokuradiyya da hadin kai na kasar.
Saboda mutane da yawa suna so su jefa kuri'u, shi ya sa an jinkirtar da yawan lokacin jefa kuri'u na wasu wurare.(Kande Gao)
|