
Ran 15 ga wata, a Dar Es Salaam, fadar mulkin kasar Tanzania, gwamnatin wucin gadi ta kasar Burundi ta kulla yarjejeniyar tsgaita bude wuta da dakaru masu adawa da gwamnatin mai taken kungiyar 'yantar da al'umma, wato Force for National Liberation a bakin Turawa.
Bayan da Domitien Ndayizeye, shugaban kasar Burundi, da Agathon Rwasa, shugaban dakarun da ba sa ga maciji da gwamnati, suka yi zantawa, Therence Sinunguruza, ministan harkokin waje na kasar ya sanar da cewa, bangarorin 2 sun tsagaita wuta nan da nan, kuma za su kafa wata kungiya a cikin wata daya domin tabbatar da tsarin tsagaita wuta. Mista Sinunguruza ya yi nuni da cewa, bangarorin 2 za su yi shawarwari kan mayar da kungiyar 'yantar da al'umma daya daga cikin bangarori masu kula da aikin shimfida zaman lafiya a kasar Burundi. (Bello)
|