Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-13 10:18:22    
Firayin ministan kasar Somaliya ya ce za a komar da gwamnatin kasar cikin gida kafin karshen watan nan

cri

Ran 12 ga wata, Mohammed Ali Ghedi, firayin ministan mai rikon kwarya na kasar Somaliya ya sanar da cewa, za a komar da gwamnatin wucin gadi ta kasar a cikin gida daga kasar Kenya kafin karshen watan Mayu mai karewa.

Bisa shirin komar da gwamnati da majalisar dokoki ta kasar Somaliya ta zartar a ran 11 ga wata, an ce, da farko, za a komar da gwamnatin kasar zuwa Baidoa da ke yammacin kasar da Jawhar da ke kuduncin kasar wadanda suka fi kwanciyar hankali, daga baya kuma, za a kaurar da ita zuwa Mogadishu, fadar mulkin kasar, sannu a hankali.

Ban da wannan kuma, bida labarin da muka samu, an ce, majalisar dokokin kasar Somaliya ta yarda da sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU da su shiga cikin kasar Somaliya. Kafin aka komar da gwamnatin kasar cikin gida, kungiyar Au za ta girke sojoji a cikin kasar, yadda za a kwatar da kurar da ta tashi. (Bello)