
Bozize shugaban kasar na yanzu
Ran 8 ga wata an gama babban zabe na karo na biyu na majalisa da na shugaba na kasar Afirka ta Tsakiya cikin lumana.
An fara babba zabe na karo na biyu a karfe 6 da safe, kuma an gama a karfe 4 da yamma, an kafa tashar jefa kuri'a 4100, mai jefa kuri'a ya kai milliyan 1.5. kuma za a bayar sakamakon babban zabe bayan mako biyu.
Bozize shugaban kasar na yanzu da Ziguele tsohon firayin minista sun shiga Gasar babban zabe na shugaban kasar. [Musa]
|