Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-06 21:53:13    
An yi hasashen cewa za a kayyade annobar ciwon zazzabin ha'bo na cutar Marburg a kasar Angola

cri
A ran 5 ga wata ministan kiwon lafiya na kasar Angola Mr. Sebastiao Veloso ya shelanta a birnin Luanda cewa, tun daga ran 4 da rana zuwa ran 5 da rana ga wata, wato cikin sa'o'i 24 da suka wuce, ba a ga bullowar sabon matsalar annobar ciwon zazzabin ha'bo na cutar Marburg a duk fadin kasar Angola. Wannan ya alamanta cewa, mai yiyuwa ne a cikin 'yan kwanakin nan mai zuwa za a iya kayyade annobar ciwon da ya yadu a duk fadin kasar Angola a cikin rabin shekarar da ta gabata.

A wannan rana, lokacin da yake karbar ziyarar da wakilin wani gidan rediyo mai hoto na kasar ya yi masa, Mr. Veloso ya ce, cutar Marburg ta kan boye a cikin jikin wani mutum har kwanaki 21. Sabo da haka, idan a cikin kwanaki 21 masu zuwa ciwon nan bai zai bullo ba, gwamnatin Angola za ta shelanta cewa ta riga ta kayyade annobar ciwon. Amma bisa labarin da abin ya shafa da aka bayar ya tsamo maganar wani jami'in hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa cewa, dole ne idan ba za a gani sabuwar bullowar ciwon a cikin kwanaki 42, za a iya shelanta cewa an kayyade ciwon nan.

Ya zuwa ran 4 ga watan Mayu, wannan annobar ciwon zazzabin ha'bo na cutar Marburg da ya bullo a arewacin kasar Angola a watan Oktoba na shekarar bara ya riga ya sa sanadiyyar mutuwar mutane 277 a kasar. (Sanusi Chen)