Ran 5 ga wata, sojojin kasar Uganda sun ba da sanarwa cewa, cikin watan Afrilu da ya gabata, an bindige dakaru 28 na kungiyar Lord's Resistance Army ta kasar.
Kakakin sojojin kasar Uganda ya ce, cikin yakin da aka yi a Kitgum da Pader da ke arewacin kasar, sojojin Uganda sun bindige dakarun kungiyar LRA 28, da ceci mutane 95 da aka yi garkuwa da su, da kuma kwace makamai da harsashi da miyagun magani da yawa. Sauran dakaru 12 na kungiyar sun ba da kai ga sojojin gwamnati. Daya daga cikin sojojin gwamnati ya rasa ransa, yayin da wasu daga cikinsu sun ji rauni. (Bello)
|