A ran 5 ga watan nan, a birnin Buenos Aires, shugaban kasar Argentina Nestor Kirchner ya gana da shugaban kasar Angola Mr. Dos Santos da yake yin ziyara a kasar. Shugabannin kasashen biyu sun yi kira da a ci gaba da karfafa hadin kai tsakanin MERCOSUR da SADC.
A cikin ganawar da aka yi, Mr. Kirchner ya darajanta muhimmiyar rawa da shugaban kasar Angola Mr. Dos Santos ya taka kan sa aya ga yakin basasa na kasar Angola cikin dogon lokaci da kuma neman samun zaman lafiya da dimokuradiyya a kasar. Ban da wannan kuma Mr. Kirchner ya bayar da sanarwar cewa, ba da dadewa ba gwamnatin kasar Argentina za ta kafa ofishin jakadancin kasar a birnin Loanda, babban birnin kasar Angola.(Kande Gao)
|