Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-06 16:02:29    
Gwamnatin Sudan ta yi kira ga dakaru masu yin adawa da gwamnatin na Darfur da su sake yin shawarwarin zaman lafiya tsakaninsu da gwamantin

cri

A ran 5 ga watan nan, mataimakin shugaban kasar Sudan na farko Mr. Taha ya yi kira ga dakaru masu yin adawa da gwamnatin na shiyyar Darfur da ke yammacin kasar Sudan da su sake fara yin shawarwarin zaman lafiya tsakaninsu da gwamnatin kasar.

Mr. Taha ya yi wannan kirari ne a gun wani taron da aka shirya a shiyyar Darfur ta arewa kan karfafa daidaituwa da hadin gwiwa a tsakanin kabilu. Shugabannin kabilun kasar Sudan da jami'an gwamnatin Sudan da kuma wakilan Amurka da Faransa da kawancen kasashen Afirka sun halarci taron. A gun taron, Mr. Taha ya yi kira ga dakaru masu yin adawa da gwamnatin na shiyyar Darfur da su fitar da kansu daga tarihi da kuma mai da hankali a kan nan gaba, bugu da kari kuma ya jadadda cewa, muddin a yi tattaunawa a tsakaninsu, sai a iya fitar da mawuyacin halin da ake ciki. Ban da wannan kuma Mr. Taha ya yi bayani cewa, gwamnatin kasa Sudan ta mai da hankali sosai kan sake yin shawarwarin zaman laifya tsakaninta da dakaru masu yin adawa da gwamnatin na shiyyar Darfur domin tabbatar da samun zaman lafiya da zaman karko a kasar.(Kande Gao)