Ran 3 ga wata, a birnin Nairobi, babban birnin kasasr Kenya, Ali Mohammed Ghedi, firayin ministan kasar Somaliya ya bayar da wata sanarwa, inda ya yi nuni da cewa, fashewar bom da aka yi a ran nan a birnin Mogadishu ba za ta hana aikin komar da gwamnatin kasar Somaliya cikin gida ba, gwamnatin za ta koma gida cikin sauri, yadda za a mayar da oda da kuma ja gorar aikin sake gina kasa.
Cikin sanarwar, an ce, yawancin jama'ar kasar Somaliya suna goyon bayan shirin komar da gwamnatin cikin gida. Amma wasu dakaru sun ki yarda da shirin bisa son kansu. Suna yunkurin hana kungiyar AU da ta tura sojojin wanzar da zaman lafiya zuwa kasar Somaliya, ta yadda suka kara tsanantar da halin da ake ciki a Mogadishu.
Duk da haka, gwamnatin wucin gadi za ta koma gida cikin sauri bayan da sojojin kungiyar AU suka isa kasar Somaliya, gwamnatin kasar Somaliya ba za ta canja niyyar da ta dauka na mayar da zaman lafiya a kasar Somaliya ba. (Bello)
|