A ran 3 ga watan nan, a birnin Yamoussoukro, babban birnin siyasa na kasar Cote d'Ivoire, firayim ministan gwamnatin hadin gamin gambiza ta kasar Cote d'Ivoire Seydou Diarra ya shugabanci taron yin nazari da tattaunawa na duk fadin kasar wanda sojojin gwamnatin kasar da dakaru masu adawa da gwamnatin suke halarta domin tabbatar da jadawalin aiwatar da shirin kwance damarar dakaru da sake kafa sojojin gwamnatin.
Mr. Diarra ya yi jawabi a bikin budewar taron, cewa ya yi maraba da bangarori daban daban na matsalar kasar Cote d'Ivoire da su bi yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba hannu a kai a watan Afril na shekarar nan a birnin Pretoria da ke kasar Afirka ta Kudu. Kuma ya yi nuni da cewa, taron shi wani muhimmin mataki ne wajen aiwatar da yarjejeniyar, haka kuma gudanar da shirin kwance damarar dakaru wani mihimmin mataki ne a cikin yukurin shimfida zaman lafiya a kasar Cote d'Ivoire.(Kande Gao)
|