Ran 3 ga wata, wani jami'in rukunin musamman na MDD da ke Liberia ya tabbatar da cewa, rukunin musamman ya riga ya fara yin bincike kan sojojin wanzar da zaman lafiya da aka zarge su da wulakantar da mata a wurin.
Bisa labarin da muka samu, rukunin musamman ya riga ya samu kai kara musu yawa game da wulakantar da mata da wasu sojojin wanzar da zaman lafiya suka yi, kuma ya samu tabbacin shaidu game da al'amura ban kunya 4.
Jami'an rukunin musamman suna nuna cewa, MDD za ta yanke hukunci ga sojojin wanzar da zaman lafiya masu aikata laifin wulakantar da mata. (Bello)
|