Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-05-04 10:25:00    
Kasar Uganda za ta jinkirtar da girke sojojin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya

cri

Ran 3 ga wata, gwamnatin kasar Uganda ta bayar da sanarwa cewa, za ta jinkirtar da girke sojojin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya.

Cikin sanarwar, an ce, sabo da kin amincewa da dakarun kasar Somaliya suka nuna, gwamnatin kasar Uganda ta yanke shawarar dakatar da lokacin da za a girke sojoji a kasar Somaliya. Bangaren Uganda ta jaddada cewa, dalilin da ya sa za a tura sojojin wanzar da zaman lafiya da suka hada da sojojin kasar Uganda da na kasar Sudan zuwa kasar Somaliya, shi ne domin neman ba da taimako kan komar da gwamnatin kasar Somaliya cikin gida. Amma mawuyacin halin da ake ciki a kasar Somaliya ba ya yarda a yi haka.

Ban da wannan kuma, bida labarin da muka samu, an ce, cikin makon nan mai karewa, Yoweri Museveni, shugaban kasar Uganda, kuma shugaban kungiyar bunkasuwa ta tsakanin gwamnatoci ta IGAD, zai gana da tawagar dakarun kasar Somaliya, inda za su yi musanyan ra'ayoyi kan maganar girke sojojin Uganda a kasar Somaliya. (Bello)