
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Chad suka watsa an ce, ciwon bakon dauro da ya fara yaduwa a farkon bana a kasar Chad yana ci gaba da yaduwa, mutane dubu 6 sun kamu da ciwon nan, guda 115 na cikinsu sun riga mu gidan gaskiya
Domin hana yaduwar ciwon nan gwamnatin Chad tana ba da allurar rigakafin ciwon nan a duk kasa baki daya, kuma tana ba da maganin kyauta ga wadanda suka kamu da ciwon nan. (Dogonyaro)
|