
Wani babban jami'in gwamnatin kasar Habasha mai kula da ayyukan ba da agaji na gaggawa ya bayyana a ran 1 ga watan nan, cewa ya zuwa yanzu mutane 112 sun mutu a cikin hadarin ambaliya da ya faru a gabashin kasar Habasha.
Kuma ya yi nuni da cewa, kusan mutane dubu 105 na jihar Somali da ke gabashin kasar suna fama da hadarin ambaliyar, kuma saboda ana shata ruwan sama yanzu, shi ya sa mai yiwuwa ne yawan masu fama da hadarin zai karu. Ban da wannan kuma ya ce, yanzu gwamnatin kasar tana cikin shirin kafa dokar-ta-baci a shiyyar. Amma saboda sharudan da aka kayyade, shi ya sa da wuya ana samar da kayayyakin agaji ga masu fama da hadarin masu yawa.(Kande Gao)
|