|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-04-29 13:52:02
|
Jam'iyyun 'yan hamayya na Cote d'Ivoire sun yi maraba da shigar da shugabanninsu a babban zabe da shugaban kasar ya amince
cri
Jam'iyyun 'yan hamayya da rukunonin dakarun 'yan hamayya na kasar Cote d'Ivoire sun ba da sanarwar hadin gwiwa a ran 28 ga watan nan cewa, sun yi maraba da kudurin da shugaban kasar Laurent Gbagbo ya tsai da, wato ya yarda da 'yan takarar neman zaman shugaban kasar na dukan jam'iyyun da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 2003, musamman ma shugaban babbar jam'iyyar 'yan hamayya Alassane Ouattara da su shiga babban zaben shugaban kasar a watan Oktoba na shekarar da muke ciki.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, aikin yunkurin shimfida zaman lafiya da sulhuntawa a kasar Cote d'Ivoire ya kawar da wani muhimmin matsala ne saboda kudurin da Mr. Gbagbo ya tsai da.(Tasallah)
|
|
|