Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-04-28 09:56:36    
Ofishin jakadan Afirka ta kudu dake wakilci a Sin ya taya murnar cikon shekaru 11 da kasar ta sami zaman walawa

cri

A ran 27 ga wata,ofishin jakadan kasar Afirka ta kudu dake wakilci a kasar Sin ya yi walimar murnar bikin kasa a nan birnin Beijing don taya murnar cikon shekaru 11 da kasar Afirka ta kudu ta sami zaman walawar dimokuradiya.

Mutane wajen 300 da suka zo daga ma`aikatar harkokin waje ta kasar Sin da ma`aikatar tsaron kasa da ofisoshin jakadun kasar Afirka ta kudu da sauran kasashe sun halarci walimar nan da aka shirya.

A ran 27 ga watan Afrilu na shekara ta 1994,an yi karo na farko na babban zaben duk kasa a kasar Afirka ta kudu,inda aka zabi Mr. Nelson Mandela wanda ya nuna kiyayya ga tsarin wariyar kabila na farar fata da ya zama shugaba na farko na sabuwar kasar Afirka ta kudu.Saboda haka ne aka mayar da ran 27 ga watan Afrilu a matsayin ranar zaman walawa ta kasar.

A ran 1 ga watan Janairu na shekara ta 1998,kasar Sin da kasar Afirka ta kudu sun kulla huldar diplomasiya a hukunce.(Jamila Zhou)