A ran 26 ga wata, a birnin Abidjan, hedkwatar tattalin arzikin kasar Cote d'Ivoire, shugaban kasar Laurent Gbagbo ya sake bayyana cewa, Cote d"Ivoire tana tsayawa tsayin daka a kan manufar kasar Sin tak a duniya, kuma yana goyon bayan gobobi biyu na zirin Taiwan da su yi shawarwari a kan neman dinkuwar kasar Sin cikin ruwan sanyi tun da wuri.
Mr.Gbagbo ya yi wannan bayani ne a gun bikin bai wa gwamnatin Cote d"Ivoire kyautar kayayyakin gidan waya da gwamnatin kasar Sin ta yi. Ya ce, yawancin kasashe sun amince da kasar Sin daya tak a duniya, kuma kasar Sin ta ba da misali mai kyau wajen daidaita maganar Hongkong da ta Macao, ya kamata ta bi hanya daya wajen daidaita maganar Taiwan.
|