|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-04-27 12:14:32
|
Za a bai wa shugaban 'yan hamayya dukkan damar shiga zaben shugaban kasar Cote d'Ivoire
cri
A ran 26 ga wata, shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo ya bayar da wani jawabi ta telebijin, inda ya bayyana cewa, zai yi amfani da ikon da doka ta 48 ta tsarin mulkin kasa ta baiwa shugaban kasar, don daukar matakan musamman, ta yadda za a baiwa shugaban 'yan hamayya Alassane Ouattara dukkan damar shiga zaben shugaban kasar da za a yi a watan Oktoba mai zuwa.
Bisa doka ta 35 ta tsarin mulkin kasar Cote d'Ivoire, tilas ne iyayen dan takarar neman zama shugaban kasar Cote d'Ivoire sun kasance 'yan kasar. Shugaban 'yan hamayya Alassane Ouattara ya riga ya rasa damar shiga zabe har sau biyu sabo da wani daga cikin iyayensa ba mutumin Cote d'Ivoire ba ne.(Lubabatu Lei)
|
|
|