
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Angola da Kungiyar WHO sun ba da rahoto kan annobar ciwon zazzabin ha'bo na cutar Marburg a ran 21 ga watan nan da dare, inda aka bayyana cewa, ba a kara samun mutumin da ya kamu da wannan ciwo a kasar Angola a cikin awoyi 24 da suka gabata ba, an sassauta annobar Marburg a kasar.
Rahoton ya bayyana cewa, ba a kara samun mutumin da ya kamu da irin wannan ciwo ba a lardunan Luanda da Cabinda da Cuanze Sul da Cianze Norte da Malanje da kuma Zaire a cikin kwanakin nan 4 da suka wuce a jere, an sassauta ciwon a wuraren nan.
Yanzu masana 40 a fannin aikin likitanci daga kungiyar WHO da kungiyar da ake kira 'doctors without borders' a turance suna ba da taimako ga ma'aikatar kiwon lafiya ta lardin Uige wajen yaki da annobar Marburg.(Tasallah)
|